IQNA

Gwamnatin Masar Ta Sanar Da Dakatar Da Sayar Da Iskar Gas Ga Haramtacciyar Kasar Isra’ila

19:14 - April 24, 2012
Lambar Labari: 2311979
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Masar ta sanar da dakatar da sayar da iskar gas ga haramtacciyar kasar Isra’ila a wani mataki da ake ganin kamar zai faranta akasarin mutanen kasar wadanda suke tsananin adawa da wannan harmtacciyar kasar, duk kuwa da cewa wasu na dangata hakan da siyasa kawai.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gwamnatin kasar Masar ta sanar da dakatar da sayar da iskar gas ga haramtacciyar kasar Isra’ila a wani mataki da ake ganin kamar zai faranta akasarin mutanen kasar wadanda suke tsananin adawa da wannan harmtacciyar kasar, duk kuwa da cewa wasu na dangata hakan da siyasa kawai.

Ministar ma'aikatar kula da hudar jakadanci da kasashe da cibiyoyi a kasar Masar ta furta cewar akwai yiyuwar kasar Masar ta sake kulla yarjejeniyar sayar da iskar gas ga haramtacciyar kasar Isra'ila a kan farashi mai tsoka.
Fayza Abu Naga ministar ma'aikatar kula da hudar jakadanci da kasashe da cibiyoyi na ciki da wajen kasar Masar a jiya litinin ta bada labarin cewar kasar Masar a shirye take ta sake kulla wata yarjejeniyar sayar da iskar gas ga haramtacciyar kasar Isra'ila a kan sabuwar kima da babu cutuwa ga kasar Masar.
Fayza ta jaddada cewar tabbas gwamnatin Masar ta rusa yarjejeniyar sayar da iskar gas da aka kulla a baya tsakanin hambararriyar gwamnatin Husni Mubarak da haramtacciyar kasar Isra'ila. Matakin da gwamnatin Masar na yanzu ta dauka na rusa yarjejeniyar sayar da iskar gas ga haramtacciyar kasar Isra'ila ya faranta ran al'ummar kasar, saboda a baya kasar Masar tana sayar da iskar gas ne a wulakantaccen farashi ga h.k.Isra'ila.
992169



captcha