Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, gasar motocin formula 1 da ake gudanarwa a kasar Bahrain na fuskantar gagarumar matsalka a akasar Bahrain sakamakon zanga-zangar da al’ummar kasar ke gudanrawa domin neman sauyi da kuma hakkokinsu da aka haramta musu lamarin da ya sanya wasu daga cikin masu gasar janyewa.
A yau dubun dubatar fararen hula sun gudanar da zanga-zanga lumana a birnin Manama na kasar Bahrain domin tabbatar wa mahukuntan kasar cewa suna nan daram kan bakansu na neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa daruruwan 'yan sandan kasar sun afka kan masu zanga-zangar da bugu da kulake da watsa musu hayaki mai sanya hawaye, wamda ke dauke da sanadarai masu guba, lamarin da ya yi sanadiyar shakewar lumfashin daruruwan fararen hula.
Masu zanga-zangar sun yi ta rera taken yin Allawadai da masarautar kasar kan matakan da take dauka na yin amfani da karfi domin hana al'ummar kasar neman hakkokinsu da aka haramta musu, inda 'yan gidan sarauta da masu dangantaka da sun e kawai suke amfana da dimbin arzikin da Allah ya huwace wa kasar, kamar yadda su ne kadai suke da hakkin rike duk wani matsayi na siyasa a kasar.
992025