IQNA

Masu Kishin Islama Sun Yi Na’am Da Dakatar Da Sayar Wa Isra’ila Iskar Gas

21:47 - April 26, 2012
Lambar Labari: 2312647
Bangaren kasa da kasa, masu kishin islama a kasar Masar sun yi na’am da matakin da mahukuntan kasar suka dauka na dakatar da sayar da islar Gas ga haramtacciyar kasar Isar’ila wanda suka jima suna kokawa a kansa tsawon shekaru.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, masu kishin islama a kasar Masar sun yi na’am da matakin da mahukuntan kasar suka dauka na dakatar da sayar da islar Gas ga haramtacciyar kasar Isar’ila wanda suka jima suna kokawa a kansa tsawon shekaru wanda tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar ya kulla cinikin sama da shekaru ashirin da ‘yan kai da suka gabta.
Haramtacciyar kasar Isra’ila ta haramtawa kiristocin kasar Masar shiga zuwa ziyara abirnin Qods mai alfarma saboda canjin siyasar da aka samu a kasar Masar a cikin wannan lokaci bayan hambarar da tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar wanda ya ke dasawa da yahudawa da Amurka gami da gwamnatin wahabiyawan saudiyya.
Wani labarin kuma daga Masar ya yi nuni da cewa, karon farko za a fitar da jaridar mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa wadda kuma za ta fara fito nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Bayanin ya ci gaba da cewa jagoran jam’iyyar Gadir ta kasar Masar kumababban sakataren majalisar koli ta mabiya tafarkin iyalan gidan manzon allah a kasar masar Muhammad Duraini shi ne ya bijiro da batun bude wannan jaridar, kuma zai bayar da gagarumar gudunmawarsa domin ci gabanta.
Wannan dai shi ne karon farko da za a fitar da wata jarida ta mabiya mazhabar iyalan gidan manzon allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa tsarkaka mai sunasautin Alilbait wanda cibiyar muslunci ta Algadir za ta dauki nauyin bugawa a kasar ta Masar.
992774


captcha