Bangaren kasa da kasa:taron kasa da kasa na karawa juna sani da kuma binciken sanin halin da al'ummar yankin Zirin Gaza ke ciki kuma za a gudanar da wannan taron ne a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar a ranar goma ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma hukumar tuntubar juna a tsakanin kasashen musulmi da musulmi ta shirya.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: taron kasa da kasa na karawa juna sani da kuma binciken sanin halin da al'ummar yankin Zirin Gaza ke ciki kuma za a gudanar da wannan taron ne a birnin Alkahira fadar mulkin kasar Masar a ranar goma ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya kuma hukumar tuntubar juna a tsakanin kasashen musulmi da musulmi ta shirya.An nakalto daga majiyar labarai na gwamnatin hadediyar daular larabawa Wam cewa: wannan taron kasa da kasa an shirya shi ne da burin sanin halin da kuncin da al'ummar yankin zirin gaza da aka killace ke ciki na kumci da matsaloli barkatai ta fuskar kiwon lafiya musamman a daidai wannan lokaci da yankin ke ciki na rikice rikice da tashin hankali da kuma uwa uba killacewa da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta yi wa al'ummar wannan yanki duk da kiraye kirayen da wasu gwamnatoci da kasashe masu dan yanci da hukumomi da kungiyoyi da kuma daidaikun mutane ke yi amma sun yi kunnan uwar shegu da lamari. Idan wannan taron zai bayyana irin matsalolin da al'ummar yankin zirin gaza ke ciki kuma a magance yanada matukar amfani amma sai dai tuni wasu na shaku kan yadda za a iya taimakwa al'ummar wannan yanki matukar haramtacciyar kasar isra'ila da manyan kasashe da ke goyan bayanta musamman Amerika bas u amince ba.
992978