Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na Iba cewa, gudanar da gasar motoci ta formula 1 da masarautar kasar Bahrain ke yi ya kara jawo fushin al'umma domin hakan tamkar wulkanta rayukan muitanen da mahukuntan kasar suka kashe ne da tozarta su a a idon duniya ta yadda wasu daga cikin kasashen da suke baiwa masautar kariya suke kokarin boye ta'asar da take tafkkawa ta hanyar halartar wannan gasa.
A nata bangaren kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka kan mahukuntan kasar Bahrain, dangane da yadda suke yin amfani da karfi kan fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasar.
A cikin wani bayani da kungiyar ta Amnesty International ta fitar a daren jiya ta sheda cewa, abin da mahukuntan kasar Bahrain ke yi ya yi hannun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa, kuma ba za a amince da ci gaban hakan ba. Kungiyar ta ce tana da karin bayanai da suke tabbatar da cewa mahukuntan Bahrain sun tafka laifuka na cin zarafin 'yan dam a kasar, da hakan ya hada da azabtar da fursunonin siyasa da yi musu kisan gilla, da dai sauran laifuka makamantan haka.
Kungiyar ta ce ya zama wajibi kan masarautar Bahrain ta gaggauta sakin dukkanin fursunonin siyasa da take tsare da su, kuma ta kame dukkanin jami'an tsaron da suka ci zarafin fararen hula masu zanga-zangar lumana a kasar, da wadanda ake tsare da su a gidan kaso.
994601