IQNA

Yahudawan Sahyuniya Sun Kafa Tutarsu A kan Rufin Masallacin Annabi Ibrahim

17:40 - April 29, 2012
Lambar Labari: 2314512
Bangaren kasa da kasa, yahudawan sahyuniya yan kaka gida sun kafa wata tutar haramtacciyar kasar isra'ila kan rufin masallacin annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi a hankoronsu na kafa tsarin yahudanci da mamaye dukaknin wurare masu tsarki da yankin.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine info cewa, yahudawan sahyuniya yan kaka gida sun kafa wata tutar haramtacciyar kasar isra'ila kan rufin masallacin annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi a hankoronsu na kafa tsarin yahudanci da mamaye dukaknin wurare masu tsarki da yankin na palastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan.
Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta dauke fursinonin Palasdinawa 140 daga inda take tsare da su zuwa wani wurin da ba'a sani ba,Shafin yanar gizo mai suna "Quds Net" ya nakalto Ahmad Al-Baitawa jami'in wata cibiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasar, yana cewa sojojin yahudawan sahyoniyya sun dauke Palasdina 140 wadanda suke yajin cin abinci daga kurkukun Majdu a safiyar yau talata zuwa wani wuri wanda har yanzub basu sani ba.
Al-Baitawi ya kara da cewa, dukkan furisinonin da sojojin suka canza masu wuri yan kungiyoyin Hamas da kuma rundunar kwatar 'yencin Palasdinawa ne, kuma daga cikinsu akwai Ahmad Alhaj Ali wani dan a majalisar dokokin Palasdinawa, tn ranar 17 ga watan Afrilu da muke ciki ne, da dama daga cikin fursinonin Palasdinawa wadanda suke tsare a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra'ila suka fara yajin cin abinci don tilasatawa gwamnatin haramtacciyar kasar ciki bukatunsu.
994818



captcha