IQNA

Keta Alfarmar Kur'ani Mai Tsarki Ya Tabbatar Da Tasananin Gaba Kan Musulunci

22:56 - May 02, 2012
Lambar Labari: 2317268
Bangaren zamantakewa, keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wani jutum mai kiran kasa malamin addinin kirsita ya yi a kasar Amurka ta tabbatar da tsananin gabar da yake yi addinin muslunci da kuma akidarsa ta nisantar addinin kirista.



Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, shugaban kwamitin kula da harkokin al'adu da ilimi na majalisar Iran Iran Haddad adil ya bayyana cewa, keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wani jutum mai kiran kasa malamin addinin kirsita ya yi a kasar Amurka ta tabbatar da tsananin gabar da yake yi addinin muslunci da kuma akidarsa ta nisantar addinin kirista wanda hakan ke tabbatar da cewa bai fahimce shi ba.

A bangare guda kuma jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah Sayyid Ali Khameni ya kirayi al'ummar kasar da su fito domin gudanar da zaben 'yan majalisa na cike gurbi da za a gudanar a ranar Juma'a mai zuwa a kasar.

Ayatollah Sayyid Ali Khameni ya yi wannan kira ne yau a lokacin da yake ganawa da dubban malaman makarantu da na jami'ion kasar a nan birnin Tehran, inda ya jaddada cewa a kowane lokacin al'ummar Iran a farke suke, kuma suna gudanar da duk wani aiki na safke wajibi domin daukakar addininsu da kasarsu da al'ummarsu, saboda haka a ranar juma'a za su fito domin tabbatar wa duniya cewa suna nan daram kan bakansu na goyon bayan tsarin Islama ta hanyar kada kuri'arsu a zaben cike gurbin kujerun majalisa.

A bangare gudana kuma ya yi bayani na jan hankali ga malaman makarantu da na jami'oi da su ci gaba da safke nauyin da ya rataya kansu na ilmantar da al'umma, domin kuwa da ilimin da suke bayarwa ne kasar da kuma al'ummarta ta kai ga matsayin da take a yau na ci gaba. 997314
captcha