Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nkalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Safir News cewa, kai hari makabartun mabiya addinin muslunci da wasu tsageru suka yi a akasar faransa wata alama ce da ke tabbatar da irin fahimta ta dabbanci a da ke cikin kwakwalen mutanen kasar dangane da addinin muslunci wanda kuma wannan ba shi ne karon farko da hakan ta faru ba.
A wani labarin kuma Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ya kirayi kasashen Sudan da kuma Sudan ta kudu da su kawo karshen tashin hankalin da suke yi a cikin sa'oi 48 masu zuwa tare da warware matsalolinsu cikin watanni uku, ko kuma su fuskanci takunkumi.
A zaman da kwamitin tsaron ya gudanar yau, dukkanin mambobinsa 15 sun amince dad a kiran kasashen Sudan da kuma Sudan ta kudu da su kawo karshen tashin hankali a tsakninsu a cikin kwanaki biyu masu zuwa, tare da gudanar da zaman tattaunawa karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afirka.
Wasu daga cikin kasashen yammacin sun bukaci amincewa da a kakaba takunkumi kan kasashen biyu, amma Rasha da China sun tsaya kai da fata domin ganin an tilasta su komawa kan teburin tattaunawa kafin daukar duk wani mataki na kakaba takunkimi. 997580