IQNA

Keta Alfarmar Kur’ani Ya Zama Hanyar Neman Matsayi A Kasashen Turai

16:36 - May 03, 2012
Lambar Labari: 2317602
Bangaren siyasa, keta alfarmar kur’ani mai tsarki ya zama wata hanya ta kamfe na siyasa da neman matsayi a cikin kasashen turai ta yadda duk mai son ya fito da kansa a matsayin wani gwarzo sai ya fara cin zarafin musulmi da keta alfarmar abubuwa masu tsarki a cikin wannan addini.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, keta alfarmar kur’ani mai tsarki ya zama wata hanya ta kamfe na siyasa da neman matsayi a cikin kasashen turai ta yadda duk mai son ya fito da kansa a matsayin wani gwarzo sai ya fara cin zarafin musulmi da keta alfarmar abubuwa masu tsarki a cikin wannan addini mai tsarki, wanda ke shiryar da dan adam zuwa ga sahihin tafarki na rayuwa.
Wani labarin kuma ya habarta cewa, yanzu haka ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmi.
A halin yanzu akwai limaman masallatai sama da dubu takwas a fadin kasar Jmaus, kuma akasarinsu mutanen kasar Turkiya dasuke je kasar daga bangaren gwamnatin Turkiya, wadanda ba su da cikakkiyar masaniya kan harshen jamusanci da ake magana da shi a kasar.
998293




captcha