IQNA

Kur’ani Mai Tsarki Na Nufin Hadadden Littafin Wahayi Daga Furkan Kuma Bayanin Da Ya Kunsa

Bangaren fikira, kur’ani mai tsarki yana nufin littafi da ya hada wahayin ubangaji ga manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka amma idan aka ce furkan hakan yana nufin bayanin ayoyinsa da kuma abin da suka kunsa da koyarwa.
A zantawar da ta hada kamfanin dillancin labaran iqna da daya daga cikin malaman addinin musuluncia jamhuriyar musulunci Muhammad Taqi Fali ya bayyana cewa, kur’ani mai tsarki yana nufin littafi da ya hada wahayin ubangaji ga manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, amma idan aka ce furkan hakan yana nufin bayanin ayoyinsa da kuma abin da suka kunsa da koyarwa na daga ilmomi da hukunce-hukunce da dai sauran duk abin da wannan littafi mai tsarki ya kunsa.
Malamin ya ci gaba da cewa, wannan littafi yana dauke da ayoyi da suke dauke hukunci da kuma kisooshi na annabawan Allah da salihan bayi, haka nan kuma yana dauke da ayoyi da suke magana kan mutanen da suka yi girman kaia bayansa kasa da kuma yadda makomarsu ta kasance domin hakan ya zama aya ga sauran al’uumomi, musamman wadanda suka kafirce ma Allah madaukakin sarki.
Fa’ali ya ce kur’ani mai tsarki yana nufin littafi da ya hada wahayin ubangaji ga manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka amma idan aka ce furkan hakan yana nufin bayanin ayoyinsa da kuma abin da suka kunsa da koyarwa, daka cikin ayoyinsa kuwa akwai masu bukatar bayani, da kuma wadanda ba su bukatar bayani. 997780