IQNA

Kungiyar WEA Ta Yi Kakkausar Suka Kan Kone Kur’ani Mai Tsarki

16:34 - May 03, 2012
Lambar Labari: 2317608
Bangaren kasa da kasa, gamayyar kungiyoyin farar hula a kasashe musulmi ta WEA ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wani mtum mai kiran kansa kirista ya yi a kasar Amurka da sunan fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi.
Kamfanin diallncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Tribune cewa gamayyar kungiyoyin farar hula a kasashe musulmi ta WEA ta fitar da wani bayani da a cikinsa ta yi kakkausar suka da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wani mtum mai kiran kansa kirista ya yi a kasar Amurka da sunan fadar albarkacin baki ko bayyana ra’ayi wanda gwamnatin Amurka da sauran gwamnatocin kasashen turai ba su uffan a kansa ba.
John Cobis wakilin musamman na majalisar dinkin duniya a kasar Afghanistan ya bukaci da hukunta dukkanin wadanda suke da hannu a keta alfarmar kur’ani mai tsarki a kasar tare da kiran kungiyar tsaro ta NATO da ta gaggauta yin hakan domin kawo karshen wutar rikicin da hakan ya jawo.
Jami’in ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Kabul na kasar, inda ya ce hakika abin da ya faru keta alfarmar kur’ani ne wanda kuma hakan ko shakka babu keta alfarmar duk wani musulmi ne aduniya, daboda hakan wadanda suka yi wannan mummunan aiki ne suke da laifi, kuma hukunta ne su kawai zai kawo karshen bala’in da hakan ya jawo a kan nato da dakarunta a kasar Afghanistn.
A cikin wani bangaren jawabin nasa ya bayyan acewa, farmakin da masu zanga-zanga cikin fushi suka kai kan ofisoshin majalisar dinkin duniya a yankin Kanduz, ya sanya su barin yanki ba arziki, amma dag abisani za su koma domin ci gaba da ayyukansu a yankin.

998393



captcha