Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-manar ta kasar Lebanon cewa, kungiyar ‘yan ta’adda da jahat Nusra ce ke da alhakin kaddamar da harin ta’addanci a cikin birnin Damascus fadar mulkin kasar Syria wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla sha daya wasu da dama kuma suka samu raunuka da sunan yunkurin neman sauyi a kasar.
Kasashen duniya da dama sun yi Allawadai da kaddamar da wannan hari, da dama daga cikin masana sun ammanar cewa kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun kawo yakin basasa a cikin kasar Syria, ta yadda hakan zai baiwa haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da cin karenta babu babbaka a yankin wadda kuma take fuskantar barazana daga kasasar ta Syria a kowane lokaci saboda matsayinta na kishin al’ummar larabawa.
Kasar Syria ita kadai ce daga cikin kasashen larabawa da haramtacciyar kasar Isra’ila take kallonta a mtasyin barazana, saboda haka faduwar Bashar Asad babbar riba ce gare tasaboda yin hakan zai ba ta damar ci gaba da aiwatar da abin da tashirya na samar wanoi sabon yanayi a yankin gabas ta tsakiya baki daya, ta yadda za ta zama babbar daula mai cikakaen iko kan sauran dukaknin kasashen yankin.
Masana da dama sun yi imanin cewa kasashen yammacin turai na hankoron ganin sun kawo yakin basasa a cikin kasar Syria ta hakan zai baiwa haramtacciyar kasar Isra’ila ci gaba da cin karenta babu babbaka a yankin wadda kuma take fuskantar barazana daga kasasar ta Syria a kowane lokaci kamar dai yadda alamu suke nuni.
998280