IQNA

An Kafa Wata Sabuwar Jam’iyyar Musulunci Ta Kurdawa A kasar Turkiya

19:05 - May 03, 2012
Lambar Labari: 2317650
Bangaren kasa da kasa, an kafa wata sabuwar jam’iyyar musulunci ta kurdawa mai suna jamiyarr muslunci ta Kurdustan kamar yadda wani daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa daga ‘yan kabilar Kurdawa na kasar Turkiya ya fada a cikin wani jawabi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na yuksekovahakaabr cewa, an kafa wata sabuwar jam’iyyar musulunci ta kurdawa mai suna jamiyarr muslunci ta Kurdustan kamar yadda wani daya daga cikin fitattun ‘yan siyasa daga ‘yan kabilar Kurdawa na kasar Turkiya ya fada a cikin wani jawabi da ya fitar da sunan jam’iyyar.
A bangare guda kuma a wani labarin na daban, ma’aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Syria ta sanar cewa ta dauki nauyin rubutawa tare da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki mai tsarki wanda shi ne irinsa na farko a kasar da nufin kara fito da matsayin kur’ani a kasar wadda daya ce daga cikin kasashen musulmi da sukee taka gagarumar rawa wajen yada addinin musulunci.
Bayanin ya ci gab ada cewa wannan kur’ani na daga cikin muhimman ayyukan da wannan ma’aikata ta gudanar a cikin tarihinta, domin kuwa za a mayar da shi ta wata hanya da dukaknin muslumin kasar za su iya amfana da shi ta hanyoyi masu sauki, kamar saka shi a cikin na’urori na musamman da suke aiki da na’ura mai kwakwalwa, ta yadda za aiya karantawa da sauraren sauti.
Ma’aikatar kula da harkokin muslunci ta kasar Syria ta sanar cewa ta dauki nauyin rubutawa tare da buga wani kwafin kur’ani mai tsarki mai tsarki wanda shi ne irinsa na farko a kasar da nufin kara fito da matsayin kur’ani a kasar wadda a koda yaushe take kokaein ta samar da hanyoyin bunkasa fahimtar musulunci.
998407


captcha