Kamfanin dillanbcin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rayo nur cewa, a kasar Lebanon ana ci gaba da yin Allawadai da keta alfarmar kur’ani mai tsarki da makiya addinin musulunci suke yi akasar Amurka da ma wasu daga cikin kasashen turai wanda hakan ke tabbaatar da irin tsananin adawar da suke yi da wannan addini mai girma.
Mutanen kasar Tunisia sun gudanar da wani gagarumin gangami domin kare martabar kur’ani mai tsarki a birnin Tunis fadar mulkin kasar tare da halartar dubban mutane daga bangarori daban-daban na al’ummar kasar wadda keda mutane sama da miliyan sha daya, kuma akasarinsu musulmi.
A nata bangaren ma’aikatar kula da harkokin addini ta kasar Tunisia ce ta sanar da hakan, wanda kuma zai ci gab aa kowace shekara, kasantuwar canjin da aka samu a kasar ba zai bayar da damar ci gaba da cin zarafin addinin muslunci kamar gwamnatin da ta gabata ba, wadda ta shara da kare manufofin kasashen yammacin turai da kuma aiwatar da su kan mutanenta.
Ranar juma’ar da ta gabata a sanar da ita a matsayin ranar kasa ta kur’ani mai tsarki a kasar Tunisia domin mayar da martani kan cin zarafi da keta alfarmar kur’ani da wani dan kasar ya yi a kawanakin baya da sunan ‘yancin fadin albarkacin baki, wanda kuma hakan wani gagarumin ci gaba da al’ummar kasar ta samu sakamakon juyin juya halin da ta yi.
998353