Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Al-alam cewa, mahukuntan kasar Bahrain sun kame daya daga cikin mambobin jam’iyyar adawa ta Amal Islami a ci gaba da daukar matakai na murkushe yunkurin da al’ummar kasar ke na neman gyara ta hanyar lumana.
Al’ummar kasar Bahrain sun fara gudanar da wata gagarumar zanga-zanga ta gama gari a duk fadin kasar mai taken nasara ko kuma shahadada nufin tabbatar wa duniya cewa suna nan kan bakansu na neman hakkkokin su babu gudu ba ja da baya kan ahkkokinsu da aka haramata musu a matsayinsu na ‘yan kasa.
Dubban daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga al’ummar kasar Bahrain a kasar Iraki, saboda tsabar zaluncin da suke fuskanta daga masarautar kama karya ta kasar, inda ake murkushe su da karfi tare da kame su da azabtar da su saboda sun nemi hakkokinsu na ‘yan kasa da aka haramta musu.
A kwanakin baya ne dai bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman hakkokinsu da aka haramta musu.
998491