IQNA

An Gudanar Ranar malamai A Seraleyon

15:49 - May 05, 2012
Lambar Labari: 2318787
Bangaren al'adu da fasaha; an gudanar da wani buki na musamman a dalilin zagayowar ranar malamai a kasar Seraleyon kuma an gudanar da wannan bukin ne a makarantar iraniyawa da ke Fritawun fadar mulkin kasar ta Seraleyon.


Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: an gudanar da wani buki na musamman a dalilin zagayowar ranar malamai a kasar Seraleyon kuma an gudanar da wannan bukin ne a makarantar iraniyawa da ke Fritawun fadar mulkin kasar ta Seraleyon. A ranar talata sha biyu ga watan Ordebeheshet na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ne aka gudanar da wannan buki kuma na samu halartar malamai da jami'an gwamnati da talibai da kuma jakadan jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan kasar da kuma uwayan yan makaranta wadanda suka jinjinawa malamai da kuma irin kokarin da suke yi wajan tarbiyartar da yayasu musamman idan aka yi la'akari da wahala da tashi fadin da ake fuskanta a wannan bangare na koyarwa.
998919
captcha