Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta yi suka dangane da ziyarar da wasu daga cikin fitatun maamai suka kai a birnin Qods tare da hadin baki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman ma babban malamin kasar Masar Ali Juma’a.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CPI cewa, kungiyar gwagwarmayar palastinawa ta Hamas ta yi suka dangane da ziyarar da wasu daga cikin fitatun maamai suka kai a birnin Qods tare da hadin baki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila musamman ma babban malamin kasar Masar Ali Juma’a wanda kuma shi ne ake yin koyi da shi a matsayin malamin addini.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.
Tafiyar da Ali Juma’a ya yi zuwa birnin Qods ya yi ne tare da hadin gwiwa da ma’aikatar tsaro ta haramatcciyar kasar Isra’ila wanda kuma ko shakka babu hakan ya sanya gagarumin shakku a cikin zukatan mutanen kasar dangane da wannan ziyara tasa, duk kuwa da cewa daga cikin abubuwan da ya yi har da duba lafiyarsa a asibiti.
Yan majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba duk kuwa da cewa bisa doka sai sun amince masa. 999476