Bangaren kasa da kasa: limamin juma'a ranar sha biyar ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain a cikin hudubar sallar juma'a a wannan ranara ya bayyana cewa: ko ana ha maza ha mata ta'addancin da gidan sarautar kasar Bahrain ke nunawa al'ummar kasar a kowace rana ta Allah ba zai kawo karshen sauyi da gawagwarmayar da al'ummar kasar ke yi ba sai ma dai abin day a ci gaba.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: limamin juma'a ranar sha biyar ga watan Ordebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Manama fadar mulkin kasar Bahrain a cikin hudubar sallar juma'a a wannan ranara ya bayyana cewa: ko ana ha maza ha mata ta'addancin da gidan sarautar kasar Bahrain ke nunawa al'ummar kasar a kowace rana ta Allah ba zai kawo karshen sauyi da gawagwarmayar da al'ummar kasar ke yi ba sai ma dai abin day a ci gaba.An nakalto daga jaridar Al'intikad da ake bugawa a kasar Labanon cewa: Ayatullahi Sheikh Isa Kasim a lokacin day a ke hudubar juma'a a masallacin juma'a na Imam sadik (AS) a yankin Diraz a birnin Manama fadar mulkin kasar ta Bahrain ya bayyana cewa; ta'addanci da muzgunawa mutane da kawo wasu canje-canje dab a su taka kara sun karya bad a gidan sarautar Ali Khalifake yin a yaudara da tsoratarwa ba zai kawo sanyin guiwa ba a kokari da gwagwarmaya da al'ummar kasar suka runguma kuma da yaradar Allah sai sun cimma manufarsu.
1000135