Bangaren kasa da kasa, daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kufah na kasar Iraki domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da ake yi a cikin kasashen yammacin turai da sunan 'yancin fadin albarkacin baki ko bayyana ra'ayi.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na aswata cewa, daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kufah na kasar Iraki domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da ake yi a cikin kasashen yammacin turai da sunan 'yancin fadin albarkacin baki ko bayyana ra'ayi wanda ake kallo a kasashen turai a matsayin demokradiyya, amma a kan kur'ani kawai ba akan akidar sahyuniyanci ba.
Bayanin ya ci gaba da cewa mutanen da suka gudanar da wannan gagarumar zanga-zanga sun yi ta rera taken mutuwa ga Amurka nasara ga musulunci, tare da kiran shugabannin kasashen musulmi da su dauki dukkanin matakan da suka dace domin kawo karshen cin fuskar da ake wa addinin muslunci da suna ra'ayi.
Rahoton ya ce daruruwan mutane sun gudanar da zanga-zanga a birnin Kufah na kasar Iraki domin nuna rashin amincewa da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da ake yi a cikin kasashen yammacin turai da sunan 'yancin fadin albarkacin baki ko bayyana mahanaga.
999936