Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa, yanzu haka ana shirin fara gudanar da wani zaman taro a mataki na duniya a birnin Alkahira na kasar Masar domin tattauna muhimman batutuwa kan matsalolin da suka addabi al’ummar musulmi a wannan zamani musamman bayan barkewar boren larabawa wanda a halin yanzu kasashen turai ke jagorancinsa tare da wasu daga cikin munafukan shugabannin larabawa ‘yan korensu.
A ranar laraba da ta gabata ce aka yi wata taho mu gama tsakanin dubban fararen hula da suke zaman dirshan a gaban ma'aikatar tsaron kasar Masar da ke birnin Alkahira, da kuma wasu daruruwan utane da suke dauke da makamai da wasu ke zargin cewa 'yan bangar tsohuwar gwamnati ne, da suke mara baya ga majalisar soji da ke mulki a kasar.
Tun a ranar Asabar din da ta gabata ce masu zaman dirshan din suka share wuri suka zauna a kusa da babban ginin ma'aikatar tsaron kasar da ke yankin Abbasiyyaa cikin birnin Alkahira, duk da irin kashedin da majalisar sojin kasar ta yi na su bar wurin, amma sun ci gaba da yin zaman dirshan din domin neman majalisar sojin kasar ta mika mulki ga hannun farar hula.
A ranar laraba wasu mutane dauke da makamai sun afka kan masu zaman dirshan din da nufin tarwatsa su da karfin tuwo, inda suka yi ba-ta-kashi, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 20 wasu da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Faruwar wannan lamari ya sanya majlaisar sojin gudanar da zaman gaggawa, domin shawo kan rikicin wanda ka iya daukar wani sabon salo da zai sake jefa kasar cikin wani mummunan tashin hankali, inda a jiya mataimakin ministan tsaron kasar ta Masar kuma mamba majalisar koli ta sojin kasar B. Janar Mukhtar Mulla ya kira taron manema labarai, inda ya sheda cewa sojoji suna nan daram kan bakansu na mika mulki ga zababben shugaban kasar Masar a ranar 30 ga watan Yunin wannan shekara.
Ya kuma kirayi masu zaman dirshan da su janye daga yankin Abbasiyya su koma dandalin Tahrir, domin kuwa a cewarsa yankin ne mai matukar muhimmanci ga harkar tsaron kasar baki daya, ya yi barazanar cewa ci gaba da zanga-zanga ko yin zaman dirshan a wurin zai fuskanci martani daga jami'an tsaro.
A nasu bangaren kungiyoyin farar hula musamman na matasa da suka jagoranci juyin da ya kawo karshen mulkin kama karya na Husni Mubarak, da kuma jam'iyun siyasa da dama, sun yi kira da a fito yau a dandalin Tahrir, domin jaddada rashin amincewa da wanzuwar sojoji kan mulkin kasar ta Masar.
Da dama daga cikin masana sun yi mannar cewa, kasashen yammacin turai gami da haramtacciyar kasar Isra'ila da ma wasu daga cikin larabawa da suke dasawa da gwamntin Husni Mubrak, sun fi fifita wanzuwar sojoji kan mulkin kasar Masar fiye da mulkin farar hula, kasantuwar masu kishin islama ne suke da rinjaye, wadanda ko shakka babu su ne za su mamaye akasarin madafun iko na kasar, wanda kasashen turai da haramtacciyar kasar Isra'ila da 'yan korensu daga cikin gwamnatocin larabawa, ba su kallon hakan a matsayin maslaha gare su.
1000459