Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na End of the American Dream cewa, bisa ga sakamakon wata kididdiga da aka gudanar a kasar Amurka an tabbatar da cewa addinin musulunci shi ne addinin da ke samun saurin karbuwa atsakanin mutanen kasar musamman ma a cikin shekarun nan na baya da gwamnatocin kasashen yammacin turai suka dauki karan tsana suka dora kan addinin muslunci.
Keta alfarmar kur’ani mai tsarki ya zama wata hanya ta kamfe na siyasa da neman matsayi a cikin kasashen turai ta yadda duk mai son ya fito da kansa a matsayin wani gwarzo sai ya fara cin zarafin musulmi da keta alfarmar abubuwa masu tsarki a cikin wannan addini mai tsarki, wanda ke shiryar da dan adam zuwa ga sahihin tafarki na rayuwa.
Wani labarin kuma ya habarta cewa, yanzu haka ana shirin gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci na kasar baki daya, wanda kuma ake ganin zai amfani matuka.
Bayanin ya ci gaba da cewa, kasar Jamus na da musulmi da yawansu ya haura miliyan hudu a fadin kasar, saboda haka wannan jami’a ta dauki nauyin bayar da karatu kan muhimman abubuwan da ya kamata masu jagorancin masallatai su koya kafin fara limanci, wanda kuma malaman addinin muslunci ne za su koyar da su a jami’a bisa tsari na karatun digiri.
Gudanar da wani shiri na musamman dangane da bayar da horo ga limaman masallatai na kasar Jamus, wanda jami’ar Snaburg ta kasar za ta dauki nauyin aiwatar da shi tare da hadin gwai da cibiyoyin mabiya addinin muslunci, hakan na da matukar alfanu ga musulmi.
1001016