IQNA

Matsaloli Na Neman hana Gudanar Da Zabe Mai Inganci A kasar Masar

12:59 - May 08, 2012
Lambar Labari: 2321260
Bangaren kasa da kasa, da dama daga cikin mutanen kasar sun shiga cikin rudani biyo bayan sabanin da ake samu tsakanin kungiyoyi da jam'iyyun siyasar kasar musamman ma bijiro da batun addini da akida inda masu rayin kishin islama su kansu sun rabu gida biyu tare da kara fito da Baraka a tsakaninsu kan harkar siyasar kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafn sadarwa na yanar gizo cewa, da dama daga cikin mutanen kasar sun shiga cikin rudani biyo bayan sabanin da ake samu tsakanin kungiyoyi da jam'iyyun siyasar kasar musamman ma bijiro da batun addini da akida inda masu rayin kishin islama su kansu sun rabu gida biyu tare da kara fito da Baraka a tsakaninsu kan harkar siyasar kasar ta Masar mai dogon tarihi.
Wata tawagar 'yan Majalisun Dokokin Kasar Masar ta gudanar da zaman tattaunawa da mambobin Majalisar Mulkin Sojin kasar da nufin neman hanyar warware rikicin da kasar take fuskanta.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewa: Tawagar 'yan Majalisun Dokokin Kasar Masar karkashin jagorancin shugaban Majalisar Sa'ad Al-Katatni sun gana da mambobin Majalisar mulkin sojin kasar a yau lahadi a kokarin da bangarorin biyu ke yi na ganin an warware matsalolin tashe tashen hankula da suke faruwa a kasar sakamakon yunkurin da al'ummar Masar ke yi na ganin an hanzarta komawa kan tsarin dimokaradiyya.
Zaman tattaunawan na yau ya fi mai da hankali ne kan batun kafa kwamitin da zai rubuta kundin tsarin mulkin kasar da rikicin da aka yi a kusa da ma'aikatar tsaron kasar Masar da ya kai ga kashe mutane biyu tare da jikkata wasu daruruwa na daban.
1001410
captcha