Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: mu'assisar da ke kula da harkokin addinin musulunci mai suna Paris Eglantine a kasar Faransa ta bada labarin wani shiri mai muhimmanci na raba kur'anai masu girma kyauta da aka rubuta da rubutun da marassa gani da gani gani kuma za a raba ne ga makaihi da masu dan gani gani. Bayan an nakalto daga majiyar labarai ta ipe08 cewa shugabannin wannan mu'assisar sun bayyana cewa: akwai mabuka masu yawa da suka gabatar da bukatarsu tab a su kur'anai da aka rubuta a cikin yaren na makaffi da msu gani gani kuma bayan wanda yak e bukata ya nuna shaidar da ke nuna cewa ya nakalci yaren makaffi yana iya karanta larabci a cikin wannan yare da kuma fahimta za a bas hi wannan kur'ani.Tuni masu lura da halin da makaffi ke ciki suka bayyana gamsuwarsu da wannan mataki kuma suke jinjinawa wannan mu'assisa da wannan mataki da ta dauka da fatar sauran mu'assshi ma su yi koyi da ita a cikin irin wannan aiki na alheri da taimakawa mabukata.
1001883