IQNA

Kungiyar Kollon Kafa Ta Nikalsit Za Ta Ginawa Garzayenta Musulmi Masallaci

17:33 - May 08, 2012
Lambar Labari: 2321538
Bangaren kasa da kasa; Alon Pardiyo mai horas da masu bugawa kungiyar kollon kafa ta Niyokastil a kasar Britaniya ya bada labarin da shugabannin wannan kungiya suka dauka da yanke shawarar ginawa fitattu da garzayenta uku musulmi masallacin da za su rika yin ibadarsu da salloli a filin was an kollon kafa na Saint Jims Park wato filin kafa mallakar wannan kungiya.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: Alon Pardiyo mai horas da masu bugawa kungiyar kollon kafa ta Niyokastil a kasar Britaniya ya bada labarin da shugabannin wannan kungiya suka dauka da yanke shawarar ginawa fitattu da garzayenta uku musulmi masallacin da za su rika yin ibadarsu da salloli a filin was an kollon kafa na Saint Jims Park wato filin kafa mallakar wannan kungiya.An jiyo daga majiyar labarai ta Goal cewa Hatam bin Arfa da ke bugawa kungiyar wasa a tsakiyar fili da kuma Pabis Sise da kuma Dambaba masu sanya kollo a raga yan aksar Senegal su uku suna daga cikin fitattun wadanda suka fi takawa kungiyar kollo a wannan shekara kuma musulmi don haka shugabannin kungiyar suka yanke shawarar gina masu masallaci kuma shugabannin kungiyar na fatar ganin a was an cin kofin kungiyoyi na Turai su taka rawar gani da ma cin nasarar lashe kofin.
1001869
captcha