IQNA

Zaman Taron Nuna Goyon Baya Ga Al’ummar Bahrain A Birnin Beirut

22:02 - May 09, 2012
Lambar Labari: 2322514
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon domin nuna cikakken goyon baya ga al’ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman mahukuntan kasar da suke samun goyon baya da daurin gindi daga gwamnatin wahabiyawan Saudiyya.
Kamfanin dilallcnin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na tashar talabijin din Almanar cewa, an gudanar da zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon domin nuna cikakken goyon baya ga al’ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman mahukuntan kasar da suke samun goyon baya da daurin gindi daga gwamnatin wahabiyawan Saudiyya da kuma uwayen gidansu na Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila.
Al’ummar kasar Bahrain sun ambaci wannan mako da suna makon yin tsayin daka a gaban azzaluman sarakunan kasar Bahrain da suke yin amfani da dukkanin karfinsu wajen murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana domin neman sauyi a cikin harkokin siyasar kasar da kuma hakkokinsu na ‘yan kasa da aka harmta musu.
Bayanin ya kara da cewa gudanar da zaman tattaunawa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon domin nuna cikakken goyon baya ga al’ummar kasar Bahrain da suke fuskantar zalunci da danniya daga azzaluman mahukuntan kasar da suke samun goyon baya da daurin gindi daga gwamnatin wahabiyawan Saudiyya da kuma uwayen gidansu na Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila, babban ci gaba ne wajen tunatar da duniya halin da Bahrain ke ciki.
1003108
captcha