IQNA

Komitin Musulmin Faransa Ya Bukacin Ladabtar Da Masu Takurawa Musulmi

13:18 - May 10, 2012
Lambar Labari: 2322707
Bangaren kasa da kasa: komitin musulmi a kasar faransa a ranar sha tara ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya bukaci shugabanni masu kula da harkokin tsaro a kasar Faransa das u ladabtar da kuma daukan mataki kan masu kai wa musulmi hari da takurawa rayuwarsu da kuma daukan matakin kama su .



Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watasa rahoton cewa: komitin musulmi a kasar faransa a ranar sha tara ga watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya bukaci shugabanni masu kula da harkokin tsaro a kasar Faransa das u ladabtar da kuma daukan mataki kan masu kai wa musulmi hari da takurawa rayuwarsu da kuma daukan matakin kama su .Bayan an nakalto daga majiyar labarai ta Atalasinfo cewa; komitin da ke kula da harkokin musulmi a kasar Faransa a matsayin na wakilin musulmi a hukumce a kasar ta Faransa bayan yin Allah wadai da babbar murya kan yadda masu tsananin nuna kama kan musulmi da addinin musulunc ke kai wa musulmi hari a biranai da kauyukan wannan kasar sun bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakai da suka dace da kuma ladabtar das u . A safiyar ranar lahadin da ta gabata ce a gaban masallacin garin Amin wasu dab a a san ko suwane ba suka kaiwa musulmi hari kuma daya daga cikin musulmin tuni yana kwance a asibici yana sha magani da yi masa jiya. Kasar Faransa na daya daga cikin kasashen turai da aka fi nuna kama kan musulmi yan asalin kasar da kuma baki da ke zaune a wannan kasa musamman a lkokacin mulkin shugaban kasar Faransa nikola Sarrkozy day a sha kayi a zaben shugabancin kasar da aka gudanar a lahadin da ta gabata.
1003719
captcha