IQNA

Yan Majalisa A Kasar Iraki Sun Bukaci Haramta Danganta Tsakanin Kasashen Musulmi Da Amerika

13:12 - May 10, 2012
Lambar Labari: 2322711
Bangaren kasa da kasa: Maha Aldauri dan majalisar dokokin a kasar Iraki ya fitar da wani bayani da a cikinsa bayan yin Allah wadai da yadda wani malamin coci ya kona kur'ani a kasar Amerika ya kuma bukaci kasashen musulmi da gwamnatocin kasashen musulmi su haramta duk wata dangantaka tsakaninsu da kasar Amerika da kuma haramta shigar kayan da aka kera a amerika shiga a cikin kasashensu domin maida martini kan wannan mataki na cin fuska kan musulmi.

Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watasa rahoton cewa: Maha Aldauri dan majalisar dokokin a kasar Iraki ya fitar da wani bayani da a cikinsa bayan yin Allah wadai da yadda wani malamin coci ya kona kur'ani a kasar Amerika ya kuma bukaci kasashen musulmi da gwamnatocin kasashen musulmi su haramta duk wata dangantaka tsakaninsu da kasar Amerika da kuma haramta shigar kayan da aka kera a amerika shiga a cikin kasashensu domin maida martini kan wannan mataki na cin fuska kan musulmi.An nakalto daga majiyar labarai ta kamfanin dillancin labarai na Aswatul Irak cewa; Maha Aldauri a cikin wannan bayani day a fitar ya bayyana cewa : kona alkur'ani mai girma da wani malamin coci ya yi a Iraki wani lamari ne da ke nuni dayadda ake kaita hurumin addinin musulunci a wannan kasa don haka ya kamata musulmi a fadin duniya su dauki matakin maida maima Amerika martini ta hanayr hadin kai da daukan mataki na bai daya da yanke duk wata dangantaka ta tattalin arziki da siyasa a tsakaninsu da Amerika da kuma haramtawa duk wani abu da ke fitowa daga amerika shiga kasashensu.
1003383
captcha