IQNA

Gwamnatin Amurka Ta Sha Alwashin Ci Gaba Da Bayar Da Makamai Ga Bahrain

13:26 - May 14, 2012
Lambar Labari: 2325550
Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin da masarautar Bahrain ke ci gaba da fuskantar bore na lumana daga al’ummar kasar domin neman sauyi a cikin dukkanin harkokin siyasa da mulki na kasar wanda ba tare da bata lokaci ba aka fara yin amfani da karfin soji a kansu yanzu kuma Amurka ta dauki alkawalin ci gaba da bayar da makamai ga wannan masarauta.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa a daidai lokacin da masarautar Bahrain ke ci gaba da fuskantar bore na lumana daga al’ummar kasar domin neman sauyi a cikin dukkanin harkokin siyasa da mulki na kasar wanda ba tare da bata lokaci ba aka fara yin amfani da karfin soji a kansu yanzu kuma Amurka ta dauki alkawalin ci gaba da bayar da makamai ga wannan masarauta ta mulkin kama karya da danne talakawa.
A bangare guda kuma bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta shiga taitayinta dangane da duk wani mataki da za ta dauka kan wannan bakar aniya.
Wanann mataki da masarautar kasar Bahrain ke neman dauka kan shehin malami baya rasa nasaba da irin kiran da yake yi ne ga mahukuntan da su saurari bukatun mutane domin warware takaddamar da ake fama da ita, maimakon yin amfani da karfin tuwo wajen murkushe fararen hula masu neman ahkkokinsu da aka haramta musu.
Bayan watsa wani labari da ke cewa masarautar kasar Bahrain na shirin kama shugaban majalisar malaman addinin muslunci ta kasar Ayatollah Sheikh Isa Kasim majalisar ta ja kunnen masarautar da ta kwana da sanin cewa, duk abin da ya samu malamin to zai kare a kanta ne.
Al’ummar Bahrain dai kamar sauran al’ummomin larabawa suna neman hakkokinsu ne da aka haramta musu ta hanyar lumana, amma mahukuntan kasar tare da na kasar Saudiyya da kuma taimakon Amurka da Birtaniya, suna ci gaba da murkushe masu zanga-zangar.
1005590

captcha