Bangaren al'adu da fasaha; hujjatul Islami Ra'is Zade ya bayyana cewa:babbar riba da mauriyar da al'ummar jamhuriyar musulunci ta Iran ta cimma daga dogaro da yin biyayya ga malami masani shi ne samin ruhin dogaro da kai da jin za su iya sun ciyar da kansu gaba ta dukan bangarori da suka hada da bangaren ilimi da fasaha da sauran fannoni daban daban na ilimi.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; hujjatul Islami Ra'is Zade ya bayyana cewa:babbar riba da mauriyar da al'ummar jamhuriyar musulunci ta Iran ta cimma daga dogaro da yin biyayya ga malami masani shi ne samin ruhin dogaro da kai da jin za su iya sun ciyar da kansu gaba ta dukan bangarori da suka hada da bangaren ilimi da fasaha da sauran fannoni daban daban na ilimi.A ranar juma'a ashirin da biyu da tawan Urdebehesht shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a daidai lokaci guda na zagayowar irin wannan rana ta haifuwar fiyayyar matan duniya fatimatul Zahra (AS) da kuma makon malamai aka gudanar da wani gagaramin taron girmamawa ga malamai day an makaranta da suka fi kwazo a fannin karatu a makarantar Afak ta kasar Labanon inda a gurin wannan taro mai muhimmanci malamai dam asana da dama suka halarci gurin taron tare da gudanar da jawabai masu gamsarwa kamar yadda fadi Nasir shugaban makarantar yayi bayani da sannu da zuwa ga baki da kuma bayani kan muhimmancin wannan rana ta Haihuwar shugabar matan duniya Fatima Zahra (AS) da kuma wannan taro na girmama malamai day an makaranta da suka yi fice a wannan mako na malamai.
1006403