IQNA

Musulmin Yankunan Kudancin Faransa Sun fara Gudanar Da Zamansu

14:54 - May 15, 2012
Lambar Labari: 2326571
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci da ke ynakunan kudancin kasar faransa sun fara gudanar da zamansu da suka yi a kowace shekara da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafe da kuma ayyukan da suke kudanarwa a kasar tare da sanbin matsaloli ko ci gaba n da suke samu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya naklato daga shafin sadarwa na yanar gizo na ramsud cewa, kungiyoyi da cibiyoyin mabiya addinin muslunci da ke ynakunan kudancin kasar faransa sun fara gudanar da zamansu da suka yi a kowace shekara da nufin tattauna muhimman batutuwa da suka shafe da kuma ayyukan da suke kudanarwa a kasar tare da sanbin matsaloli ko ci gaban da suke samu musamman ma ganin cewa an samu canjin gwamnati a kasar, bayan mulkin fir’aunancin da tsohon shugaban kasar ya yi.
A bangare guda kuma shugaban kasar Mauritania Mohammad Wuld Abdulaziz ya gana da zababben shugaban kasar Faransa Franswa Holland eta wayar tarho kan muhimman batutuwa da suka shafi alakar kasashen biyu da kuma yankin Sahel.
Kamfanin dilalncin labaran kasar Faransa ya habarta cewa, a zantawar da ta hada shugabannin biyu yau, sun mayar da hankali kan barazanar da kasar ta Mauritania da sauran kasashen yankin sahel suke fuskanta daga kungiyoyin da suke da dangantaka da kungiyar alkaida da suke dauke da makamai, da kuma jaddada wajabcin ci gaba da shiga kafar wando daya da su.
A cikin shekara ta 2010 ne gwamnatin Mauritania tare da gwamnatin Mali suka cimma yarjejeniya da kasar Faransa kan fatattakar mayakan kungiyar alkaida a arewacin Afirka, inda yanzu haka suke gudanar da ayyuka na hadin gwiwa a tsakaninsu a kan iyakokin kasashen biyu.
1007319



captcha