Bangaren siyasa da zamantakewa, shugaban cibiyar yada al’adu da bunkasa harkokin ilimin addinin muslunci ya bayyana cewa komawar mulki ga hannun masu tsatsauran ra’ayin addini da ke faruwa yanzu a wasu kasashen musulmi hakan babban baraza ce mai hadari ga duniyar musulmi baki daya.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Mohammad Baghir Khorramshad shugaban cibiyar yada al’adu da bunkasa harkokin ilimin addinin muslunci ya bayyana cewa komawar mulki ga hannun masu tsatsauran ra’ayin addini da ke faruwa yanzu a wasu kasashen musulmi hakan babban baraza ce mai hadari ga duniyar musulmi baki daya tare da bata sunan wannan addini mai tsarki.
Malamin ya ci gaba da cewa abubuwan da suke faruwa yanzu haka a cikin kasashen larabawa yana da tasiri matuka ga kishin addinin muslunci da al’ummomi suke yi, amma hakan ba ya nufin cewa abin da ke faruwa kuma shi ne daidai, domin kuwa suna yin amfani da son addinin mustane domin su karbi mulki sai kuma su wuce gona da iri wajen abin da suke ganin addini ne.
Mohammad Baghir Khorramshad shugaban cibiyar yada al’adu da bunkasa harkokin ilimin addinin muslunci ya bayyana cewa komawar mulki ga hannun masu tsatsauran ra’ayin addini da ke faruwa yanzu a wasu kasashen musulmi hakan babban baraza ce mai hadari ga duniyar musulmi baki daya, ku ci gaban hakan zai zamanto tattare da batunci ga sunan addini a nan gaba a duniya.
1007038