Bangaren siyasa da zamantakewa, wani rahoto da babbar cibioyar mabiya addinin muslunci ta kasar Jamus ta fitar ya tabbatar da cewa masu tsananin gaba da addinin muslunci na kasar da kyamar baki sun kaddamar da hare-hare kan masallatai mallakin mabiya addinin musulunci kasar sau sama ta dari biyu a cikin kimanin shekaru goma da suka gabata.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, wani rahoto da babbar cibioyar mabiya addinin muslunci ta kasar Jamus ta fitar ya tabbatar da cewa masu tsananin gaba da addinin muslunci na kasar da kyamar baki sun kaddamar da hare-hare kan masallatai mallakin mabiya addinin musulunci kasar sau sama ta dari biyu a cikin kimanin shekaru goma da suka gabata domin neman tsokanar musulmi.
Kasar Jamus dai na daga cikin kasashen da ake nuna ma musulmi banbanci da wariya tare da nuna musu kyma, duk kuwa da cewa gwamnatin kasar na kokarin ta nuna ma duniya cewa tana bin sahihin tafarkin demokradiyya tare da kare hakkokin marassa rinjaye, amma hakan bai sa musulmi sun kubuta daga sharriin makiyansu na cikin kasar ba, inda har ta kai ga wasu daga cikin jami’an gwamnatin kasar suna fitowa karara suna sukar addinin muslunci.
Rahoto da babbar cibioyar mabiya addinin muslunci ta kasar Jamus ta fitar ya tabbatar da cewa masu tsananin gaba da addinin muslunci na kasar da kyamar baki sun kaddamar da hare-hare kan masallatai mallakin mabiya addinin musulunci kasar sau sama ta dari biyu a cikin kimanin shekaru goma da suka gabata, ba tare da mahukuntan kasar sun yi komai kan hakan ba. 1007290