Bangaren siyasa da zamantakewa: ofishin da ke kula da shugabanni da darektoci na kasa masu kula da harkokin koyar da ilimin addinin musulunci da ke karkashin ma'aiaktar koyarwa da tarbiya ta jmahuriyar musulunci ta Iran a ranar ashirin da watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya aka bude rashen wannan cibiya a kasar Cote D'ivoire da ke yammacin Afrika.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: ofishin da ke kula da shugabanni da darektoci na kasa masu kula da harkokin koyar da ilimin addinin musulunci da ke karkashin ma'aiaktar koyarwa da tarbiya ta jmahuriyar musulunci ta Iran a ranar ashirin da watan Ordebehesht na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in da daya hijira shamsiya aka bude rashen wannan cibiya a kasar Cote D'ivoire da ke yammacin Afrika.Bude wannan cibiya ko shakka babu zai taimaka matuka gaya wajan bada horo da yaya malamai da wadanda nauyin tarbiyartar da yara manyan gobe ya rata a wuyansu kuma ko ba komi nan gaba za a a ci moriya da alfanon wannan lamari musamman idan aka yi la'akarin da yadda addinin musulunci ya fara shiga da kutsawa a cikin al'ummar wannan kafa ta Cote D'ivoire da yawancin al'ummominta suka kasance kiristoci .Kuma bukin kaddamar da wannan cibiya an kaddamar das hi ne a babban dakin taro na ma'aiakatar harkokin waje da ke birnin Abijan fadar mulkin kasar .
1007737