IQNA

Jami'an Tsaron Bahrain Da Na Saudiyya Sun Rusa Masallacin Abu Talib A Garin Hamad

10:29 - May 16, 2012
Lambar Labari: 2327158
Bangaren kasa da kasa, jami'an tsaron kasar Bahrain da sojojin Saudiyya ke rufa ma baya sun rusa masallacin Abu talib da ke garin Hamad a kusa da birnin Manama da nufin ci gaba da murkushe boren da al'ummar kasar ke yin a neman sauyin siyasa da mulki zuwa ga demokradiyya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-wifagh cewa jami'an tsaron kasar Bahrain da sojojin Saudiyya ke rufa ma baya sun rusa masallacin Abu talib da ke garin Hamad a kusa da birnin Manama da nufin ci gaba da murkushe boren da al'ummar kasar ke yin a neman sauyin siyasa da mulki zuwa ga demokradiyya wanda aka haramta musu tsawon shekaru.
A cikin shekarun da suka gabata kasar Saudiyya ta mayar da kasar Bahrain tamkar wata jaha daga cikin kasarta, lamarin day a sanya al'ummar wannan kasa nuna rashin gamsuwarsu da wannan salon siyasa da mahukuntan kasar ske bi inda suka sayar da kasar ga masarautar Saudiya, bayan fara boren neman sauyi, Saudiyya ta aike da sojoji da tankokin yaki domin murkushe zanga-zangar al'umma, abin da ke ci gaba da faruwa ken an a halin yanzu.
Rahoton y ace jami'an tsaron kasar Bahrain da sojojin Saudiyya ke rufa ma baya sun rusa masallacin Abu talib da ke garin Hamad a kusa da birnin Manama da nufin ci gaba da murkushe boren da al'ummar kasar ke yin a neman sauyin siyasa da mulki zuwa ga mulki na farar hula.
Majalisar shawarar Musulunci ta Iran ta yi Allawadai da kokarin da kasar saudia da Amurka suke yi na hade kasar Bahrai da ita saudia, a cikin wata sanarwa wacce yan majalisar 190 suka sanyawa hannun, majalisar ta bayyana a jiya litinin cewa, nuna karfi ba zai taba warware matsalar kasar Bahrain ba. Kuma matakin hade ita Bahrain da saudia zai kara yada rikicin ne kawai.
Tun ranar 14-Maris na shekarar bara ne dai sojojin kasar Saudia 1000 guda suka shiga kasar Bahrain don tallafawa jami'an tsaron kasar murkushe borin da mutanen kasar suke wa sarakunan kasar.
Kasar Saudia dai ta bayyana anniyarta na dunkulewarta da sauran kasashen larabawa na yankin tekun Parisa 5, wato Bahrai, Kuwait, Qatar, Hadaddiyar daular Larabawa da kuma Oman, don fuskantar abinda ta kira barazanar da suke fuskanta.
A jiya ne kasashen 6 suka gudanar da zamansu na farko a kan wannan manufar amma sun tashi ba tare da sun cimma wani abin a zo gani ba, saboda abin da wasu daga cikinsu ke kallo na cewa Saudiyya na neman mamaye su ne.
1008335
captcha