Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, a karshen wannan makon da muke ci za a gudanar da wani taron abje koli na littafan addini da kuma gwagwarmata a lokacin gudanar da bukukuwan bude sabbin gidajen da aka sake ginawa a garin Bint Jubail bayan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta rusa su a lokacin yakin kwanaki talatin da uku da ta yi da kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah inda ta sha kashi a hannun dakarun na kungiyar Allah madaukakin sarki.
A can kasar pakistan ma yanzu haka ana ci gaba da gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar an nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibviyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor, birnin na boyi ta fuskancin girma da kuma harkokin tattalin arziki na kasar Pakistan.
A wajen taron na bajen kolin an nuna kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki wadanda aka rubuta da hannu a kasashen musulmi daban-daban, haka nan kuma wadanda aka buga su a kasashen musulmi, da nufin kara fito da matsayin wannan littafi mai tsarki, tare da bayyanawa duniya cewa matsayinsa yana damfare ne da rayuwar mabiya addinin muslunci, domin ya zama hannunka mai sanda ga masu keta alfarmarsa.
Gudanar da taron baje koli na kasa da ake yi a kasar Pakistan inda ake nuna wasu daga cikin manyan kwafin kur’ani mai tsarki a ginin babbar cibiyar yada al’adun muslunci da ke birnin Lahor na kasar, na dag acikin muhimamn ayyuka da gwamnatin kasar pakistan ke aiwatarwa akowace shekara. Amma a wannan shekara lamarin ya dauki sabon salo na kara kawata taron, da kuma yawan kur’anan da ake nunawa.
1009572