IQNA

Jagoran Kiristocin Lebanon Ya Gana Da Musulmin Kasar Amurka

21:47 - May 17, 2012
Lambar Labari: 2328087
Bangaren kasa da kasa, jagoran mabiya addinin kirista na kasar Lebanon ya gana da mabiya addinin musulunci na kasar Amurkaa ziyarar aiki da yake gudanarwa yanzu haka kasar inda ya jaddada musu cewa a koda yaushe yana dakyakyawar fahimta da alaka da mabiya addinin muslunci a ko’ina cikin fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na lorientlejor cewa, jagoran mabiya addinin kirista na kasar Lebanon ya gana da mabiya addinin musulunci na kasar Amurkaa ziyarar aiki da yake gudanarwa yanzu haka kasar inda ya jaddada musu cewa a koda yaushe yana dakyakyawar fahimta da alaka da mabiya addinin muslunci a ko’ina cikin fadin duniya na ma kawai a kasar lebanon ba.
A wani rahoton kuma majalisar mabiya addinin muslunci a kasar Faransa za ta shigar da kara kan mutanen da suek nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai da suke zaune a kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa kasar Faransa na daga cikin kasashen nahiyar turai da suka fi yawan musulmi, ta yadda adadinsu ya zama su ne na biyu ta fuskacin yawa a kasar bayan mabiya addinin kiristanci, amma kuma duk da haka har yanzu gwamnatin kasar ba ta amince da addinin musulunci a hkumance ba amatsayin daya daga cikin addinain kasar, duk kuwea da cewa ta amince da addinin yahudanci.
Shigar da kara kan mutanen da suke nuna matuar adawa da addinin muslunci a kasar faransa saboda abin da suke yi na kokarin haddasa rikici da rashin fahimtar juna tsakanin mabiya addinin musulunci da sauran mabiya addainai, yin hakan zai zama tamkar wani hannunka mai sanda ga sauran masu irin wannan akida asauran kasashen turai.
1009565



captcha