Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin din Almanar cewa, wasu sun yi barazanar kashe wani bayahude masanin tarihi a haramtacciyar kasar Isra’ila saboda fitar wasu bayanai da ya yi da ke karyata cewa yankin palastinu mallakin yahudawa ne wanda hakan ya zama hujjar mamaye shi tare da korar palastinawa daga yankin, inda ya ce yin hakan zalunci ne.
Sai kuma a wani labarin al’ummar birnin paris na kasar Faransa za su gudanar da wata zanga-zangar nuna rashin amincewa da kyamar al’umar musulmi na kasar da ake yi tare da nuna musu banbanci da karan tsana wanda hakan ya yi hannun riga da duk wata dabi’a ta dan adam wanda kuma siyasar shugaban kasar na yanzu ta taimaka wajen hakan.
Wani rahoton kuma ya yi nuni da cewa wani masani kuma injiniya dan kasa Spain mai suna David Fapregat dan kasar Spain ya karbi addinin muslunci a ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran da ke birnin Madrid bayan gudanar da bincike kan addinin muslunci da koyarwarsa mai tsarki.
Wannan na daga cikin alamun da suke tabbatar da cewa al’ummomin kasashen turai suna karbar addinin muslunci a cikin wannan lokacin fiye da sauran lokutan da suka gabata, inda suke nuna matukar sha’awarsu kan addinin muslunci bayan gudanar da bincike kan koyarwarsa, da kuma yadda ake kokarin dushe haskensa a tsakanin al’ummomin da suke rayuwa a cikin wannan nahiya.
Wannan masani kuma injiniya dan kasa Spain mai suna David Fapregat dan kasar Spain da ya karbi addinin muslunci a ofishin jakadancin jamhuriyar musulunci ta Iran da ke birnin Madrid, ya tabbatar da cewa ya gamsu da addinin musulunci ne bayan ya karanta littafai da na akidunsa, wanda kuma shi ne ya yi daidai da hankali fiye da akidun kowane addini a duniya.
1009407