Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na palastine cewa, sojojin haramtacciyar kasar isra’ila sun kame kanan yara da matasa palastinawa da dama a ranar tunawa da kafa wannan haramtacciyar kasa sakamakon gudanar da zanga-zangar nuna kiyayya da wannan haramtacciyar kasa da ta ginu kan zalunci da danniya da mamaya.
Su ma wasu masu zanga-zanga a kasar Turkiya sun kone tutocin haramtacciyar kasar Isra’ila da uwar gijyarta Amurka a kasar turkiya domin nuna fushi kan kiesan gillan da da suke yi kan al’ummar musulmi a cikin palastinu da kuma kasar Afghanistan a cikin lokutannan saboda tsabar zalunci da danniya kan musulmi.
Masu zanga-zangar a cikin fushi sun banzama kan m,anyan tituna acikin birane da dama da suka hada da birnin Istanbul babbar cibiyar kasuwancin kasar ta Turkiya, kamar yadda aka gudanar da wata gagarumar zanga-zangar irin wannan a cikin birnin Ankara fadar mulkin kasar ta siyasa.
A lokutan bayaa dai kasar Turkiya ta nuna ma msuulmi kamar tana tare da lamarinsu, inda ta nuna matukar adawa ga haramtacciyar kasar Isra’ila kan batun kai hare-hare a zirin Gaza, amma daga bisani bayan da musulmi suka fada cikin tarkon da ta dana musu sai ta fitar da manufar a fili, inda a halin yanzu take ci gaba da kawancenta da yahudawan sahyuniya, kuma ba ta cewa uffan kan kisan gillar da ake yi wa fararen hula a Gaza. 1009402