Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ISESCO cewa an buga tare da fitar da mujallar ilimi da kimiyya ta kungiyar bunkasa harkokin ilimi da al’adun musulmi wadda take dauke da bayanai a wannan bangare daga masana da kuma malamai wadda ta fito a birnin Ribat fadar mulkin kasar Morocco.
A wani bayani da ya gabatar a gidan talabijin din kasar Faransa a zantawar da ta hada shi da gidan talabijin shugaban kasar Nikola Sarkozy ya bayyana cewa ba su lalae marhabin da Yusuf Qardawi bisa zarginsa da tunzura mutane wajen aikata ayyukan ta’addanci da kuma tsatsauran ra’yi, wanda a cewarsa Faransa ba ta amince da hakan ba.
Shugaban kasar ta Faransa ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wata zantawa tare da sarkin kasar Qatar wanda daya ne daga cikin amintattu ga kasar Faransa, kuma shi ne wanda ya ajiye Qardawi a kasar bayan mahukuntan Masar sun kore shi sakamakon matakan da yake dauka na tunzura mutane zuwa tsatsauran ra’ayi, wanda kuma hakan ya kawo rashin jituwa tsakanin Qatar da Masar.
A cikin ‘yan lokutan nan dai Qardawi ya fitar da fatwoyi na kafirta mutane da suka hada da fatawarsa kan Husni Mubarak a lokacin da mutane suna bore a kasar Masar, haka nan kuma ya kafirta Gaddafi da kuma shugaban kasar Syria Bashar Asad, tare da halasta jininsa, gami da yin kira da a taimaka ma ‘yan ta’adda
1009304