IQNA

An Amince Da Ayar Dokar Kudi Ta Bankin Musulunci A kasar Libya

20:56 - May 19, 2012
Lambar Labari: 2329308
Bangaren kasa da kasa, majaisar wucin gadin kasar Libya ta amince da daftarin dokar kudi karkashin tsarin bankin musulunci kamar yadda ake gudanarwa a wasu kasashen yankunan gabacin nahiyar asia da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Aljazira cewa, majaisar wucin gadin kasar Libya ta amince da daftarin dokar kudi karkashin tsarin bankin musulunci kamar yadda ake gudanarwa a wasu kasashen yankunan gabacin nahiyar asia da kuma wasu daga cikin kasashen musulmi da na larabawa da suka fara yin aiki da hakan.
Shi kuwa Mansur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi kamar yadda ake gani a duk inda suka wata kungiya ko cibiya, a cikin kasashen musulmi da ma kasashen da ba na musulmi ba.
Ya ci gaba da cewa dle ne a dauki dukaknin matakan da suka dace domin takawa ‘yan salafiyya burki kan ayyukansu na wuce gona da iri, tare da kara fadakar da mutane kan muhimmancin zaman lafiya da kuma kaurace ma su neman fitina acikin al’ummar musulmi, wanda a cewarsa hakan ne kawai zai kawo zaman lafiya a cikin al’umma.
Masur Marzuki shugaban kasar Tunisia ya yi dirar mikiya kan masu akidar salafiya na kasar da cewa suna mayar da hannun agogo baya a cikin dukaknin harkoki na siyasa a kasar tare da yada tunaninsu na neman tashin hankali da kawo fitina a cikin al’ummar musulmi, domin kawai su cimma manufofinsu, ko kuma zatra da manufofin wasu bisa sani ko bisa jahilci.
1010669

captcha