Bangaran kasa da kasa: masallacin garin Ayova a kasar Amerika ya bullo da wani shiri na musamman na yada addinin musulunci ga wadanda ba musulmi ba inda a kowace ranar juma'a zai rika bude kofar masallacin ga duk wanda yake bukata.
Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: masallacin garin Ayova a kasar Amerika ya bullo da wani shiri na musamman na yada addinin musulunci ga wadanda ba musulmi ba inda a kowace ranar juma'a zai rika bude kofar masallacin ga duk wanda yake bukata.Rahotonni da aka jiyo daga majiyar kusa da shugabannin masallacin sun bayyana cewa musulmi da ke salla a wannan masallacin ne sukabada shawarar cewa ya kamata kuma ya dace a bude kofar masallaci a bude a kowace ranar juma'a domin bawa wadanda ba musulmi bad a su kansu musulmin damar ziyartar wannan masallaci kuma hakan wata hanya ce da za ta kara kusanci a tsakanin musulmi da sauran al'ummomi wadanda ba musulmi ba a wannan jaha.
1012059