IQNA

Shugaban Cibiyar Kula Da Ayyukan Addini Ya Kai Ziyara Ga Sayyid Nasrullah

21:03 - May 21, 2012
Lambar Labari: 2331065
Bangaren kasa da kasa, shugaban cibiyar kula da ayyukan addini a jamhuriyar muslunci ta Iran kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci ya kai wata ziyara ga babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullah tare da tawagarsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, godan talabijin Almanar na kasar Lebanon da ke birnin Beirut ya habarta cewa, a jiya shugaban cibiyar kula da ayyukan addini a jamhuriyar muslunci ta Iran kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci ya kai wata ziyara ga babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullah tare da tawagarsa dake rufa masa baya, daga cikinsu har da jakadan jahuriyar mulunci a kasar Lebanon.
Wannan ganawa ta tabo abubuwa da dama da suka hada da dangataka tsakanin kungiyar hizbullah da kuma kasar Iran, da yadda ake samun gagarumin ci gaba a dukaknin fuskoki tsakanin kasashen Iran da Lebanon, wanda hakan ke kara tabbatar da cewa kasashen biyu suna da mahanga guda da ta hada su, ita ce ‘yancin siyasa da kuma zama cikin fadaka da karfafa alaka a tsakaninsu.
Muhammad Muhammadi shugaban cibiyar kula da ayyukan addini a jamhuriyar muslunci ta Iran kuma wakilin jagoran juyin juya halin muslunci ya kai wata ziyara ga babban sakataren kungiyar gwagwarmaya ta hizbullah a kasar Lebanon Sayyid Hasan Nasrullah tare da tawagarsa, inda suka gana a gidansa da ke birnin Beirut.
1011883


captcha