IQNA

Bijiro Da Batun Hade Bahrain Da Saudiyya Mamaye Ce Ba Hadewa Ba

13:00 - May 22, 2012
Lambar Labari: 2331588
Bangaren kasa da kasa, makircin da mahukuntan kasar Saudiyya gami da karnukan farautarsu an kasar Bahrain suka shirya da nufin mayar da kasashen biyu cikin kasa guda wato Saudiyya hakan mamaya ce ba wai hadewa ba kamar yadda bangaroin biyu suke son nuna ma duniya.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta shi da daya daga cikin fitattun ‘yan adawar Bahrain Muhammad kazim Shahabi ya bayyana cewa, makircin da mahukuntan kasar Saudiyya gami da karnukan farautarsu an kasar Bahrain suka shirya da nufin mayar da kasashen biyu cikin kasa guda wato Saudiyya hakan mamaya ce ba wai hadewa ba kamar yadda mahukuntan kasashen biyu suke bayyanawa ba.
A daya bangare kuma kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya yi kakkausar suka dangane da cin zarafin dan adam da mahukuntan kasar Bahrain key i, ta hanyar yin amfani da karfi wajen murkushe al’ummar kasar da suke neman sauyi a cikin harkokin siyasa da mulkin kasar ta hanyar lumana.
A lokacin da kwamitin yake gudanar da zamansa a jiya a birnin Jeneva na kasar Switzerland, tare da halartar dukaknin wakilan kasashe 47 mambobin kwamitin, da ma wakilan manyan kungiyoyin kare hakkin bil adama nakasa da kasa, da suka hada da Amnesty International da kuma Human Rights Watch, kwamitin ya nuna matukar damuwa dangane da yadda mahukuntan Bahrain suke keta alfarmar ‘yan dam.
Dukkanin mahalarta taron dai sun yi amannar cewa, abin da mahukuntan Bahrain suke yi azabtar da masu neman sauyi da jagororin kare hakkin bil adama na kasar, hakan yay i hannun riga da dukaknin dokoki na kasa da kasa, a kan haka suka kirayi masarautar Bahrain da ta gaggauta gudanar da bincike kan kisan gillar da jami’anta suka yi wa fararen hula masu zanga-zangar lumana, da kuma azabtar da dubban mutane da aka yi a cikin gidajen kason kasar saboda ra’ayoyinsu na siyasa, tare da sakin dukaknin fursunonin siyasa, da suka hada da tsohon shugaban cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar Abdulhadi Al-khawajah, wanda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai, saboda ra’ayinsa na siyasa.
Tun acikin watan Fabrairun shekara ta 2011 ne al’ummar kasar Bahrain suka fara gudanar da zanga-zangar lumana domin neman sauyi a cikin tsarin siyasa da mulkin kasar, inda suka bukaci sarki ya I gaba da rike matsayinsa na sarauta, amma ya gudanar da canje-canje ta hanyar bayar da dama ga mutane su zabi gwamnati da kansu, ta hanyar zaben ‘yan majalisa, wadanda su kuma za su zabi pira minista da kuma rubuta kundin tsarin mulki wanda al’ummar kasar za ta amince da shi, maimakon sarki ya zama shi ne mai nada ‘yan majalisa da pira minista, tare da bayar da dukkanin madafun iko ga ‘yan gidan sarauta kawai ko kuma masu dangataka da su.
Maimakon yin dubi ga abin da al’ummar Bahrain suka bukata, sarkin kasar tare da hadin gwiwa da gwamnatin Saudiyya sun yi amfani da karfin soji da na ‘yan sanda wajen murkushe mutanen kasar, domin rufe bakunansu kan wadannan sauye-sauye da suke bukata, inda har yanzu masarautar kasar tare da gwamnatin Saudiyya bas u gushe ba suna ci gaba da murkushe wannan yunkuri na lumana ba, duk kuwa da cewa Amurka da Birtaniya da kuma Haramtacciyar Kasar isra’ila suna da hannu kai tsaye wajen murkushe yunkurin al’ummar Bahrain na neman sauyi. 1012987
captcha