IQNA

Za A Nuna Wata Makala Kan Jami'ar Musulunci Ta Rasha

Bangaren al'adu da fasaha; bayan kammala wata ziyarar aiki da wata tawagar gidan talbijin ta kasar Malaishiya ta gudanar a jami'ar musulunci ta kasar Rasha da ke birnin Kazan fadar mulkin jamhuriyar Tataristan an cimma matsaya guda ta shiryawa da nuna wata makala kan wannan jami'a da gidan Talbijin din na Malaishiya zai nuna.

Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin da suka shafi kur'ani mai girma a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa: bayan kammala wata ziyarar aiki da wata tawagar gidan talbijin ta kasar Malaishiya ta gudanar a jami'ar musulunci ta kasar Rasha da ke birnin Kazan fadar mulkin jamhuriyar Tataristan an cimma matsaya guda ta shiryawa da nuna wata makala kan wannan jami'a da gidan Talbijin din na Malaishiya zai nuna. Wannan makalai da nazari na Karin ilimi kan wannan jami'ar a watan azumin mai zuwa ne gidan talbijin din zai nuna kuma a lokacin wanan ziyarar tawagar gidan talbijin din na Malaishiya ya gana da Marat Gilman Uf shugaban jami'ar da kuma Ramadan Khuram Shin da Abdallah Sangara uf shugabannin bangarorin kula da koyarwa a jami'ar.Har ila yau sun samu sun gana da wasu daga cikin malaman da ke koyarwa a wannan jami'ar da kuma wasu daga cikin yan jamiar da ke karatu a wannan jami'a ta musulunci ta kasar Rasha.
1013069