Bnagaren kasa da kasa, da dama daga cikin amsu bin diddigin lamurran siyasar kasar Masar suna hasashen cewa dan takarar kungiyar Ikhwanul musulmin ne zai lashe zaben shugaban kasar wanda aka fara gudanarwa a yau laraba kuma za a sanar da sakamakonsa na karshen bayan ‘yan kwanaki masu zuwa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na tashar talabijin din Alalam cewa, da dama daga cikin amsu bin diddigin lamurran siyasar kasar Masar suna hasashen cewa dan takarar kungiyar Ikhwanul musulmin ne zai lashe zaben shugaban kasar wanda aka fara gudanarwa a yau laraba kuma za a sanar da sakamakonsa na karshen bayan ‘yan kwanaki masu zuwa kamar dai yadda sakamakon jin ra’ayin jama’a ya nuna.
Bisa ga sakamakon jin ra’ayin dan takarar kungiyar Ikhwan shi ne zai lashe zaben da samun kuri’u masu rinjaye, daga shi kuma sai dan karar da ya ballae daga kungiyar, wanda kuma ya tsaya takarar ne a matsayin mai cin gishin kansa ba karkashin kungiya ba ko wata jam’iyya, to amma kuma bisa la’akari da cewa mutane suna zaben kungiya ne ko jam’iyya ba mutum bisa la’akari da shirinsa da kuma manufarsa ba, wannan ya sanya ake hasashen cewa ikhwan za su lashe.
Masu bin diddigin lamurran siyasar kasar Masar suna hasashen cewa dan takarar kungiyar Ikhwanul musulmin ne zai lashe zaben shugaban kasar wanda aka fara gudanarwa a yau laraba kuma za a sanar da sakamakonsa na karshen bayan ‘yan kwanaki, gami da wani dalilin da yake kara tabbatar da hakan wato sakamakon zaben waje da aka gdanar. 1015088