Bangaren kasa da kasa, a daidai lokacin makircin masarautar saudiyya ya ci tura na yunkurin hade Bahrain da Saudiyya su zama kasa daya domin kawo karshen yunkurin mutanen kasar na neman sauyi wannan ya sanya gwamnatin saudiya da ita kanta Bahrain neman taimakon haramtacciyar kasar Isra’ila a hukumance domin murkushe masu neman sauyi ta hanyar lumana.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a daidai lokacin makircin masarautar saudiyya ya ci tura na yunkurin hade Bahrain da Saudiyya su zama kasa daya domin kawo karshen yunkurin mutanen kasar na neman sauyi wannan ya sanya gwamnatin saudiya da ita kanta Bahrain neman taimakon haramtacciyar kasar Isra’ila a hukumance domin murkushe masu neman sauyi ta hanyar lumana, domin kuwa sun yi amfani da dukkanin karfinsu wajen kashe su da kawo karshensu amma abin ya ci tura.
Shugaban kwamitin amintattu na majalisar malaman kasar Bahrain Ahmad Zain ya sheda cewa shigar da sojojin mamayar kasar saudiyya suka yia acikin kasar Bahrain domin murkushe fararen hula masu zanga-zangar lumana da neman hakkokinsu da aka haramta musu ya yi hannun riga da dukaknin dokokin kasa da kasa, da ma dokokin kasar ta Bahrain.
A bangare guda kuma kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci a gudanar da bincike akan kisan da jami'an tsaro su ka yi wa wani mai zanga-zanga a gabacin saudiyya, a wani bayani da kungiyar ta kare hakkin bil'adama ta fitar ta bukaci a yi bincike mai zaman kanshi akan kisan da aka yi wa Isam Muhammad Abu Abdullah a lokacin da ya ke cikin zanga-zanga a garin Awamiyyah da ke gabacin kasar.
1014896