Bangaren kasa da kasa, babban mai shigar da kara a kasar Saudiyya ya bukaci da yanke hukuncin kisa kan lauyan nan dan kasar Masar wanda mahukuntan Saudiyya suka kame shi akwanakin baya alokacin da yaje gudanar da ibadar Umra bisa wani zargi da ake shakku a cikinsa kan cewa yana dauke da kwayoyi da aka haramta a kasar.
Kmafanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar yaum sabi cewa babban mai shigar da kara a kasar Saudiyya ya bukaci da yanke hukuncin kisa kan lauyan nan dan kasar Masar wanda mahukuntan Saudiyya suka kame shi akwanakin baya alokacin da yaje gudanar da ibadar Umra bisa wani zargi da ake shakku a cikinsa kan cewa yana dauke da kwayoyi da aka haramta a kasar wadda ke ikirarin aiki da kur'ani, amma da dama daga cikin masu lamarin suna ganin matakin na siyasa ne kawai.
Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi suka da kakkausar murya akan yadda ake murkushe 'yan hammayya a cikin kasar Saudiyya, a cikin rohotonta na shekara-shekara kungiyar ta Amnesty ta ce: "Yunkurin da al'ummar Saudiyya din su ke yi wanda ya samo asali ne daga abinda ya ke faruwa a cikin sauran kasashen yankin, ya fuskanci murkushewa mai tsanani daga mahukuntan kasar.
Kungiyar ta Amnesty International ta ci gaba da cewa: " Mahukuntan na Saudiyya sun kame mutane masu yawan gaske mafi yawancinsu masu kare hakkin bil'adama wadanda su ka rika nuna kin amincewarsu a shekarar da ta gabata ta 2011, kungiyar kare hakkin bil'adaman ta ci gaba da cewa: Da akwai dubban mutane a cikin gidajen kurkukun saudiyya kuma suna fuskantar azabtarwa da kuma cin zarafi.
1016091