IQNA

Tarukan Tunawa Da Ranar Shadar Ayatollah Sayyid Baqir Hakim A Kasar Iraki

15:22 - May 27, 2012
Lambar Labari: 2335256
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da tarukan tunawa da ranar shahadar Ayatollah Bakir Hakim wanda ya rasa rayuwarsa ‘yan watanni bayan komawarsa kasar Irakia wani harin ta’addanci da mabiya tafarkin wahabiyanci suka kai kansa tare da sauran musulmi a garin Najaf mai alfarma.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na sautul iraq cewa, a jiya an gudanar da tarukan tunawa da ranar shahadar Ayatollah Bakir Hakim wanda ya rasa rayuwarsa ‘yan watanni bayan komawarsa kasar Irakia wani harin ta’addanci da mabiya tafarkin wahabiyanci suka kai kansa tare da sauran musulmi a garin Najaf mai alfarma wanda ya samu halartar dubban daruruwan mutane.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan taro da aka gudanar a Iraki shi ne irinsa na tara da aka gudanar domin tunawa da ranar shahadar babban malamin wanda ya karar da rayuwarsa wajen bin tafarkin kakaknsa da kuma salihain bayi dag cikin mabiya tafarkinsu, ya koma kasar Iraki bayan kawo karshen mulkin tsohon shugaban mulkin kama karya na kasar Iraki a wancan lokaci Saddam Hussain, wanda ya kasance yana gudun hijira ne alokacin jamhuriyar musulunci ta Iran.
An gudanar da tarukan na tunawa da ranar shahadar Ayatollah Bakir Hakim wanda ya rasa rayuwarsa ‘yan watanni bayan komawarsa kasar Iraki a wani harin ta’addanci da mabiya tafarkin wahabiyanci suka kai kansa tare da sauran musulmi a garin Najaf mai alfarma bayan kammala sallar juma’a. 1017036
captcha