IQNA

Nuna Kyama Ga Musulmi Wani Nauin Sabon Mulkin Mallaka Ne

18:56 - May 27, 2012
Lambar Labari: 2335388
Bangaren kasa da kasa, nuna tsananin kiyayya ga mabiya addinin muslunci da ake yi a halin yanzu a cikin kasashen yammacin turai musamman ma a kasar Amurka hakan wata babbar manuniya ta wani sabon mulkin mallaka da ake son yi kan al’ummomin duniya da suke son rayuwa a cikin ‘yanci.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin press TV cewa, nuna tsananin kiyayya ga mabiya addinin muslunci da ake yi a halin yanzu a cikin kasashen yammacin turai musamman ma a kasar Amurka hakan wata babbar manuniya ta wani sabon mulkin mallaka da ake son yi kan al’ummomin duniya da suke son rayuwa a cikin ‘yanci na siyasa.
Baynain ya ci gaba da cewa a halin yanzu kasar Amurka ta zama babban abun buga misali wajen nuna kiyayya da kyma ga mabiya taffarkin islama, duk kuwa da cewa addinin muslunci shi ne addinin da ya fi samun karbuwa a tsakanin al’ummomin kasar, inda a halin yanzu a ke lissafa su da miliyoyi.
Kafofin yada labarai na kasashen yammacin turai suna taka gagarumar rawa wajen karfafa gwiwar masu akidar cin zarafin musulmi da kuma keta alfarmar musulmi da addinin musulunci a duniya kamar dai yadda muke gani a duniya musamman ma a cikin nahiyar turai.
an watsa labarai masu karo da juna dangane da makomar majalisar ministocin kasar masar karkashin jagorancin fira minitsna Kamal Janzuri wanda masu tsaurin ra’yin kishin islama suke tuhumarsa da kasawa yayin da majalisar sojin kasar ba ta ba shi goyon bayn da yake bukata wajen gudanar da ayyukansa na tafiyar da mulki.
Mambobin majasar dokokin kasar Masar sun yi kira da a safke babban malamin kasar mai bayar da fatawa bayan ya yi tafiya zuwa haramtacciyar kasar Isra’ila ba tare da izinin majalisa da kuma yin shawara da majalisar malaman addinin muslunci ta kasar ba lamarin da ake kallonsa a matsayin wani babban kure.

1016629


captcha