Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa babban sakataren majalisar tsaron kasa a jamhuriyar muslunci ta Iran Said Jalili ya gudanar da tattaunawa tare da babban malamin addinin musulunci na kasar Iraki kan abubuwa da suke faruwa yanzu haka acikin duniya da kuma yankin gabas ta tsakiya tare da bayyana masa matsayin jamhuriyar muslunci a kansu, musamman abubuwan da makiya addii da al’umma suke ciki.
A bangare guda kuma daya daga cikin malaman addinin musuluncia jamhuriyar musulunci Muhammad Taqi Fali ya bayyana cewa, kur’ani mai tsarki yana nufin littafi da ya hada wahayin ubangaji ga manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka, amma idan aka ce furkan hakan yana nufin bayanin ayoyinsa da kuma abin da suka kunsa da koyarwa na daga ilmomi da hukunce-hukunce da dai sauran duk abin da wannan littafi mai tsarki ya kunsa.
Malamin ya ci gaba da cewa, wannan littafi yana dauke da ayoyi da suke dauke hukunci da kuma kisooshi na annabawan Allah da salihan bayi, haka nan kuma yana dauke da ayoyi da suke magana kan mutanen da suka yi girman kaia bayansa kasa da kuma yadda makomarsu ta kasance domin hakan ya zama aya ga sauran al’uumomi, musamman wadanda suka kafirce ma Allah madaukakin sarki.
Fa’ali ya ce kur’ani mai tsarki yana nufin littafi da ya hada wahayin ubangaji ga manzonsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalan gidansa tsarkaka amma idan aka ce furkan hakan yana nufin bayanin ayoyinsa da kuma abin da suka kunsa da koyarwa, daka cikin ayoyinsa kuwa akwai masu bukatar bayani, da kuma wadanda ba su bukatar bayani.
1016422